<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Yesu, Dutsen Cetona, bar in ƃuya wurinka.
 Jini, fansar mutane; ruwa, tsarkakewar rai,
 Ga su, suna zubowa daga cikin zuciyarka.

[V2]
 2) Hannu wofi fa na zo, jinƙanka ne na ke so.
 Dukan zuciya, dukan rai, duk ƙazanta ne kaɗai.
 Ga ni wurin giciyenka, ina neman gafara.

[V3]
 3) Kome yawan aikina, bai isa cetona ba.
 Ko ban huta ba daɗai, kullum ina hawaye,
 Dukan wannan banza ne, kai kaɗai Mai Ceto ne.

[V4]
 4) Ran da za a binne ni, ko kuwa za a fyauce ni,
 Ran da zan bar duniyan nan, Zan dai gan ka zaune can,
 Amma kamin ranan nan, bar in ƃuya wurinka.</lyrics>
<title>Yesu, Dutsen Cetona, Bar In Ɓuya Wurinka LW170</title>
<hymn_number>170</hymn_number>
<author>Paul Baloche, Hastings, Thomas (1784-1872), Toplady, Augustus Montague (1740-1778)</author>
</song>